Search This Blog

Wednesday, August 21, 2013

An kashe mutane hudu a Gamboru Ngala


Rahotanni daga garin Gamboru Ngala a jihar Borno na cewar wadansu matasa masu dauke da makamai  sunka kashe mutane hudu tare da raunata wasu Hudu.
Wani mazaunin garin, ya bayyana cewar an yi jana'izar mutane hudun sannan wadanda suka samu raunuka suna jinya a wata asibiti.
Mutumin wanda bai son ya bayyana sunansa ya ce, 'matasa masu dauke da makaman  sun yi amfani da wata dabarar janyo hankalin 'yan garin ta hanyar busa asur kafin su bude musu wuta.
Babu wata kafa mai zaman kanta da ta tabbatar da wannan labarin saboda rashin hanyar sadarwa a yanki gaba daya.
Wannan abu ya faru ne kwanaki biyu bayanda jami'an tsaro suka sanarda cewa watakila Shugaban Boko Haram, Abubakar Shekau ya mutu sakamakon raunukan da ya samu na harbin bindiga.

No comments:

Post a Comment