Search This Blog

Tuesday, August 20, 2013

An kama shugaban 'Yan Uwa Musulmi


Shugaban kungiyar 'Yan Uwa Musulmi Mohammed Badie






Kafar yada labarai ta kasar Masar ta bayanna cafke jagoran kungiyar 'Yan Uwa Musulmi, Mohammad Badie, a Alkahira babban birnin kasar.
Rahotanni sun ce ana tsare da shi a wani gida dake gabashin gundumar birnin Nasr.
Birnin na Nasr daya daga cikin manyan wuraren da magoya bayan hambararren shugaba Mohammed Morsi suka yi zaman dirshan ne, da jami'an tsaro suka tarwatsa a makon jiya, da ya yi sanadiyyar mutuwar daruruwan mutane.

Wakilin BBC ya ce cafke Mohammad Bade wata babbar mahangurba ce ga kungiyar 'yan uwa Musulmi, a wannan yanayi da mahukuntan kasar ta Masar ke bin diddigin shugabanninsu a fadin kasar.



No comments:

Post a Comment